Manyan Labarai
NDLEA za ta samar da cibiyoyin gyaran hali da tarbiyya guda 6
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA za ta kafa cibiyoyin gyaran hali da tarbiyya guda shida a shiyyoyin siyasa na ƙasar nan.
Shugaban Hukumar Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ne ya sanar da hakan a wajen taron ƙasa da ƙasa karo na 5 kan batun yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi da aka yi a Abuja.
Da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman a wajen taron, Janar Marwa ya ce “ayyukan sha da fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙaruwa a duniya musamman a nan Najeriya”.
Ya ce sakamakon wani binciken da hukumar ta UNODC ta gudanar ya nuna cewa kashi 14.4 cikin 100 ko kuma mutane miliyan 14.3 ƴyan Najeriya masu shekaru tsakanin 15 zuwa 64 suna amfani da wani sinadarin da ke da illa ga lafiyar kwakwalwa a cikin shekarar da ta gabata.
A cewar sa, wannan ne ya sanya hukumar fara ƙoƙarin dakile dabi’ar ta hanyar samar da cibiyoyin gyaran hali guda shida a shiyyoyin siyasar ƙasar nan shida a shekara mai zuwa.
Har ma ya ce guda uku daga cikin cibiyoyin za su fara aiki ne a shekara mai zuwa kamar yadda aka tsara a kasafin kudin 2022.
You must be logged in to post a comment Login