Connect with us

Labarai

NELFUND ta musanta labarin dena biyan alawus na dalibai

Published

on

Asusun Bayar da Lamunin karatu na kasarnan NELFUND, ya musanta rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa an dakatar da biyan kuɗin alawus ga ɗaliban da ke cin gajiyar shirin lamunin karatu na Gwamnatin Tarayya na zangon karatu na shekarar 2025/2026.

Mai magana da yawun asusun, Oseyemi Oluwatuyi, ta ce takardar da ake yaɗawa ba daga NELFUND ta fito ba, kuma babu wata sanarwa da gwamnati ko asusun suka fitar game da dakatar da biyan alawus. Ta ƙara da cewa ana ci gaba da biyan kuɗin makaranta da na alawus ga waɗanda suka cancanta kamar yadda tsarin shirin ya tanada.

NELFUND ta buƙaci ɗalibai da iyaye da su dinga tantance sahihancin duk wani bayani ta hanyoyin sadarwa na hukuma kafin su yaɗa shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!