Connect with us

Labarai

PDP ta bukaci gwamnan Kwara ya ceto mutane 176 da aka sace a Woro

Published

on

Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kwara ta bukaci Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kara kaimi wajen ganin an ceto mata da yara 176 da aka sace daga kauyen Woro da ke karamar hukumar Kaiama tun ranar 3 ga Fabrairu, 2026. Jam’iyyar ta ce nasarar da aka samu wajen kubutar da dalibai da malamai da aka sace a jihar Oyo ta nuna cewa hadin gwiwa da jajircewar gwamnati na iya haifar da sakamako.

 

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran PDP na jihar, Olusegun Adewara, ya fitar, jam’iyyar ta yabawa Gwamna Seyi Makinde bisa rawar da ya taka wajen kubutar da wadanda aka sace a Oyo. Ta ce mutanen Woro sun shafe kwanaki 158 a hannun masu garkuwa da mutane, tana zargin gwamnatin Kwara da rashin nuna isasshen himma wajen ceto su.

 

Jam’iyyar ta kuma zargi gwamnatin jihar da muzgunawa masu sukar ta maimakon mayar da hankali kan magance matsalar tsaro, tare da kira ga ‘yan jarida, kungiyoyin farar hula da sauran al’umma su matsa wa gwamnati lamba domin a ceto sauran mutanen da ke hannun ‘yan bindiga. Sai dai gwamnatin jihar Kwara ba ta fitar da martani ba kafin lokacin wallafa rahoton.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!