Labarai
NEMA na horas da masu ruwa da tsaki wajen kulawa da asarar rayuka
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta jaddada aniyarta ta inganta kwarewar masu ruwa da tsaki kan kula da asarar rayuka.
Yayin da yake kaddamar da fara horas da masu ruwa da tsaki yadda za a rage yawan asarar rayuka, Babban Daraktan hukumar, Mr Mustapha Ahmed, yayi kira da a rinka girmama lokaci tare da nuna kwarewa wajen bada agajin gaggawa.
NEMA ta shirya bayar da horon ne tare da hadin kan Ofishin mai ba da shawara kan tsaro na kasa (ONSA), ya kuma samu tallafi daga Babban Ofishin Burtaniya da Ofishin Jakadancin Amurka.
Ahmed, ya ce, horon zai baiwa wadanda suka samu halartar damar samun sabbin dabaru da kwarewa da karawa juna sani da kuma sabbin dabarun ceton rayukan al’umma yayin afkuwar iftila’I.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Ahmed ya bukaci masu ruwa da tsaki da su yi amfani da ilimin da suka samu daga wannan horon don bayar da gudummawa wajen rage samun nakasassu da mace-macen jama’a, wanda aka fi samu sakamakon manyan iftila’I.
You must be logged in to post a comment Login