Labarai
NEMA ta shawarci gwamnoni su kafa cibiyoyin ba da agajin gaggawa
Hukumar ba da agajin gaggawa NEMA, ta shawarci gwamnonin Nijeriya da su kafa kananan cibiyoyin ba da agajin gaggawa, tare da karfafa ayyukan hukumomin ba da agaji na jihohinsu domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa a damunar bana.
Darakta Janar na hukumar Mustapha Habib Ahmad, ne ya bayar da shawarar a ganawarsa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, bayan kammala ganawa da kungiyar gwamnonin Nijeriya NGF.
Mustapha Habib, ya ce, akwai bukatar gwamnonin su dauki wannan mataki domin dakile afkuwar annobar ambaliyar ruwa da ke addabar wasu jihohi da dama.
Haka kuma, Ya kara da cewa matukar gwamnonin suka hada kai da hukumar NEMA, to hakika akwai yiwuwar rage tasirin barnar da amlabiyar ruwa ke yi da kaso mai girma.
You must be logged in to post a comment Login