Kiwon Lafiya
NEMA:gwamnatin tarayya ta kai dauki ga al’ummar jihohin Adamawa da Taraba
Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bukaci gwamnatin tarraya da ta kai dauki ga al’ummar jihohin Adamawa da Taraba, sakamakon rikicin ‘yan-tada kayar baya da rikicin kabilanci.
Babban darakta na hukumar Akube Iyawu ne ya bayyana haka, yayin zantawa da manema labarai, a babban birnin Yola na jihar Adamawa.
Akube Iyawu ya kuma ce, sun zo Jihar ne don ganiwa idanun su barnar da jihohin biyu suka samu sakamakon tashe-tahsen hankalin a sassan Jihohin.
Akube Iyawu ya kuma ce, al’ummar jihohin na bukatar agajin don kuwa yawancin su, sun rasa dokiyoyinsu da dama, hadi da matsugun-nansu baya ga rashin zaman lafiya da ke adabar jihohin