Labarai
NEMA:ta bayyana cewa baraguzan gini a Jihar Legas ya kashe mutum biyu

Rahottani daga jihar Lagos na nuni da cewa akalla yara biyu ne suka rasa rayukansu a wani gini da ya rufta a titin Ajao a unguwar Ikorodu a jihar.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA ta ce ‘lamarin ya faru ne da safiyar jiya Asabar’.
Hukumar ta Kuma ce ba a samu kai agajin gaggawa ba a kan lokaci don ceto rayukan yaran.
Gidan talabijin nan Channels ya ruwaito cewa, ‘Hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas ta ziyarci wurin da lamarin ya faru domin tantance lamarin’.
You must be logged in to post a comment Login