Kiwon Lafiya
NERC: ta ce samar da meter wutar lantarki alhakin kamfanonin DISCOS ne
Hukumar kula da harkokin samar da wutar lantarki ta kasa (NERC), ta ce samar da meter wutar lantarki ga masu amfani da wuta, lamari ne da ya rataya a wuyar kamfanonin rarraba wutar lantraki wato Discos.
A cewar hukumar, hakan ya yi daidai da dokar samar da mita ta shekarar da ta gabata ta dubu biyu da goma sha takwas wato ’’Meter Asset Provider Regulations 2018’’.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta NERC ta fitar, ta ce, kafin bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki lasisi, sashe na hudu daya cikin baka na dokar; ta ce, samar da meter wutar lantarki hakki ne da ya rataya a wuyar kamfanonin rarraba wutar lantarki.
Hukumar kula da harkokin samar da wutar lantarkin ta cikin sanarwar dai, ta ce tana mai da martani ne kan wata sanarwa da kungiyar masu kamfanonin rarraba wutar lantarki ta kasa wato Discos suka fitar a baya-bayan nan cewa, yanzu ba su ke da hakkin samar da meter wutar lantarki ga jama’a ba.
Sanarwar ta kara da cewa, tun farko dokar ta ce ana saran kamfanonin rarraba wutar lantarki su fara aikin samar da meter ga mabukata ne cikin wa’adin kwanaki dari da ashirin da fara aikin su.