Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NFPL: Gombe United ta doke Kano Pillars

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tayi rashin nasara a hannun Gombe United da ci daya da nema a gasar Firimiya ta kasa da suka fafata.

Filin wasa na Pantami shi ne dai ya karbi bakuncin wasan da ya gudana a ranar Lahadi 03 ga Afrilun 2022.

Dan wasa Barnabas Daniel ne dai ya zura kwallon a minti na 65 a karawar da aka shafe minti 90 ana bugawa tsakanin kungiyoyin da suka fito daga arewacin kasar nan.

Nasarar da Gombe United tayi ya sa ta koma mataki na 9 da maki 27 a wasanni 20 da suka fafata.

Inda kuma Kano Pillars ta kasance a mataki na 13 da maki 24 a wasanni 20 da ta buga a kakar wasannin da muke ciki ta shekarar 2021/2022.

Yanzu haka dai Rivers United itace a matakin farko da maki 43 a wasa 20 da ta fafata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!