Labarai
Ngige: Zan dauki matakin shari’a kan gwamnonin da su ka rage albashin ma’aikata
Ministan kwadago da samar da aikin yi, Sanata Chris Ngige, ya ce, tuni ya fara tuntubar atoni janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami don neman shawararsa kan daukar tsastsauran mataki kan jihohi wadanda suke tattauna batun mafi karancin albashi da kungiyoyin kwadago na jihohinsu.
A cewar sanata Chris Ngige, lamarin zai iya kaiwa ya dauki matakin shari’a kan gwamnoni da kwamishinoninsu na kudi da kuma sauran jami’an gwmanati da suka shiga cikin harkokin neman ragewa ma’aikata mafi karancin albashin.
Ministan kwadagon ya bayyana hakan ne yayin zantawa da gidan talabijin na Channels.
Tun farko dai gamayyar kungiyoyin kwadagon sun bukaci gwamnatin jihohi da su guji ragewa ma’aikata mafi karancin albashin na naira dubu talatin wanda aka yi yarjejeniya aka amince.
You must be logged in to post a comment Login