Barka Da Hantsi
NITDA: Fasahar sadarwa na ci gaba da bunƙasa tattalin arziƙi a ƙasar nan
Hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta zamani ta ƙasa NITDA ta ce, fasahar sadarwa na taka muhummiyar rawa wujen bunkasa tattalin arziki a kasar nan da ma duniya baki daya.
Shugaban hukumar Kashifu Inuwa Abdullahi ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom radio da mayar da hankali kan gudummuwar da fasahar sadarwa ke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin.
Kashifu Inuwa Abdullahi ya ce zuwan annobar korona ya dada zaburar da mutane Wajen yin amfani da fasahar sadarwa wanda hakan ya taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arziki a kasar nan.
Kazalika ya ce, “A lokacin annobar harkokin fasahar sadarwa ya samu tagomashi, domin kuwa mafi yawan al’amura an mayar da shi kafar internet sakamakon dokar kulle”.
Kashifu ya kuma ce “Wannan ne ya sa gwamnati ta fitar da tsare tsare domin bunkasa fasahar zamani, haka kuma sabon tsarin nan na 5g zai taimaka wajen bunkasa fasahar zamani da tattalin arziki, kuma nan gaba kadan za mu dora Najeriya akai wanda tuni kasashen da suka ci gaba sun wuce wurin”.
Kashifu Inuwa Abdullahi ya ce hukumar tana bada gudummawa matuka wajen inganta harkar ilimi.
You must be logged in to post a comment Login