Connect with us

Labarai

NLC ta ayyana goyon baya ga yajin aikin da Ƙungiyar NUT ke yi

Published

on

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta ayyana  goyon bayanta ga yajin aikin da mambobin Kungiyar Malamai ta NUT ke yi a halin yanzu sakamakon  tabarbarewar tsaro da kuma yawaitar sace malamai da dalibai.

A cikin wata sanarwa da shugaban NLC, Joe Ajaero, ya fitar a Daren jiya  Laraba, ya ce yajin aikin ya nuna irin gajiyar da malamai suka yi sakamakon hare-haren da ake ci gaba da kai musu, musamman a wuraren da ke fuskantar barazanar tsaro.

Ya bayyana cewa wasu abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ciki har da sace daliban makaranta a Jihar Oyo, sun kara nuni da yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a fadin kasar nan.

Ajaero ya ce  akwai bukatar gwamnati ta dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin malamai da dalibai, tare da samar da yanayin da zai ba da damar gudanar da harkokin ilimi cikin kwanciyar hankali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!