Connect with us

Labarai

ADC ta zargi Shugaba Tinubu da nuna wariya

Published

on

Jam’iyyar ADC a Jihar Kano ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna wariya wajen tafiyar da harkokin tsaro tsakanin Arewa da Kudu.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Musa Ungoggo, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matakin gaggawar da gwamnatin tarayya ta ɗauka domin ceto mutane 40 da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo ya bambanta da yadda ake mayar da martani ga hare-haren da ke faruwa a jihohin Arewa.

Musa Ungoggo ya yi nuni da hare-haren da suka jawo asarar rayuka a jihohin Plateau, Kaduna, Sokoto, Zamfara, Katsina da Neja, yana mai cewa al’ummomin Arewa sun daɗe suna fuskantar matsalolin tsaro ba tare da samun irin kulawar da gwamnatin tarayya ta nuna a Oyo ba.

Ya kuma zargi fadar shugaban ƙasa da tafiyar da tsarin tsaro da ke fifita wasu yankuna fiye da wasu, lamarin da ya ce na iya haifar da rarrabuwar kawuna a ƙasa.

Jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya faɗaɗa irin matakan tsaron da aka ɗauka a Oyo zuwa jihohin Arewa da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya, tare da ƙara tura jami’an tsaro da masu gadin dazuka domin magance matsalar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!