Connect with us

Labarai

NLC ta nuna damuwa kan yawaitar garkuwa da dalibai

Published

on

Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, ta bukaci gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su dauki matakan gaggawa domin kawo karshen yawaitar sace yara a kasar nan. Shugaban kungiyar, Joe Ajaero, ya bayyana cewa makarantu sun fara zama wuraren kai hare-hare, lamarin da ke barazana ga makomar yara da ilimi a Najeriya.

NLC ta nuna damuwa kan sace dalibai 39 da malamai bakwai daga wasu makarantu a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo, inda ta ce rahotanni sun nuna cewa an kashe wani malami yayin da ake tsare da su. Kungiyar ta ce matsalar tsaro na kara kamari har ta kai ga babu wani yanki da ake ganin yana da cikakken tsaro.

Kungiyar ta bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen ceto wadanda aka sace, su inganta tattara bayanan sirri da kuma samar da tsaro a makarantu. NLC ta ce lokaci ya yi da gwamnati za ta dauki matakan da za su dawo da amincewar jama’a tare da kare rayukan yara a fadin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!