Connect with us

Labarai

NLC ta bukaci gwamnatin tarayya ta samar da hanyoyin saukaka hauhawar kayayyaki

Published

on

Kungiyar Kwadago ta Najeriya , NLC, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta bijiro da hanyoyin da za su samar wa da yan mutane sauki da kuma karin albashi na musamman ga ma’aikata yayin da farashin man fetur ke kara tashi.

 

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce karin farashin man fetur zai kara tsadar sufuri da abinci da sauran bukatun yau da kullum.

 

NLC ta kuma bukaci gwamnati ta tabbatar da sayar da danyen mai ga matatun cikin gida da Naira, domin rage tasirin matsalar farashin mai ga ‘yan Najeriya.

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wasu daga cikin yan kasar nan sun fara tafiya da kafa mai nisa, sakamakon tashin farashin man fetur, domin ragewa kansu kudin sufuri.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!