Labarai
NLC ta nuna kaduwar ta kan sallamar malamai a jihar Kwara
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Kwara ta nuna kaduwar ta kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na sallamar wasu malaman Firamare dubu biyu da dari hudu da goma sha hudu, wadanda tsohuwar gwamnatin jihar ta daukesu aiki.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Issa Ore, da ya fitar a jiya Laraba.
Sanarwar ta ce sallamar ma’aikata masu yawa a jihar zai kara janyo samun karin marasa aikin yi da ake dasu a jihar.
A cewar sanarwar, sallamar malaman zai kuma kawo koma baya a harkokin koyarwa a jihar ta yadda dalibai za su shiga cikin matsala na rashin wadatattun malamai.
Kungiyar ta kwadagon ta cikin sanarwar dai ta kuma soki kudirin da gwamnatin ta dauka na sallamar ma’aikatan.
Hukumar Kula da Ilimin bai daya ta jihar (SUBEB) ce ta sanar da korar malaman sakamakon zargin cewa basu cancanta ba.
You must be logged in to post a comment Login