Labarai
NLC ta zargi gwamnatin Nijeriya da gaza kawo matsaya kan batun shiga yajin aikin data shirya
Kungiyar kwadago a Nijeriya ta zargi gwamnatin tarayyar kasar da rashin shirin kawo karshen tattaunawar dake gudana a tsakani, kan aniyarsu ta tafiya yajin aiki sakamakon halin da kasar nan ke ciki dalilin janye tallafin man fetir da kuma kara masa kudi.
Wakilan kungiyar karkashin jagorancin Shugabanta na kasa kwamret Joe Ajaro sun fice daga dakin taron tattaunawar sakamakon rashin halartar kwamatocin bayar da tallafin gwamnatin tarayya wajen cimma matsaya.
Kazalika kungiyar tace gwamnatin na amfani da tarukan ne kawai don yaudarar al’ummar kasar nan, biyo bayan rashin halartar kwamatin dake wakiltar gwamnatin tarayyar a zaman.
Bangarorin biyu dai sun amince da su ci gaba da tattaunawa a ranar Juma’ar nan ne dai bayan zaman da suka gudanar a ranar Larabar da ta gabata.
Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login