Labarai
NLC:sunyi barazanar tsunduma yajin aikin gama gari
Gamayyar kungiyoyin kwadago a kasar nan sun yi barazanar sake tsunduma yajin aikin gama gari matukar aka ci gaba da samun tsaiko wajen aiwatar da shirin mafi karancin albashi na naira dubu talatin ga ma’aikatan kasar nan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mr. Anchaver Simon da kuma Alade Lawal.
Sanarwar ta kuma ruwaito gamayyar kungiyoyin na bayyana rashin jin dadin su game da jan kafa da ake samu wajen aiwatar da shirin biyan mafi karancin albashin.
A cewar kungiyoyin ta cikin sanarwar dai babu gudu ba ja da baya game da fara biyan mafi karancin albashin a dukkannin jihohin kasar nan talatin da shida.
Gamayyar kungiyoyin kwadagon sun ce tun farko sun shaidawa gwamnati cewa, tun da anyi karin sama da kaso talatin da shida a mafi karancin albashi ga ma’aikata, wanda ya tashi daga naira goma sha takwas zuwa naira dubu talatin, saboda haka wajibi ne ayi kari ga albashin ma’aikata daga Matakin Grade Levels 01 zuwa Grade Levels 017.