Labarai
NMA: Rashin tsaftar muhalli na kawo yaduwar cutar Covid-19
Kungiyar likitoci ta kasa reshan jahar kano NMA ta bayyana cewar rashin tsaftar muhalli a tsakanin al’umma ke kara yaduwar cutar corana da ake fama da ita a fadin Duniya.
Shugaban kungiyar Dakta Sanusi Muhammad Bala ne ya bayyna hakan jim kadan bayan kammala shirinn barka da hantsi na nan tashar freedom radiyo.
Ya kuma ce akwai bukatar al’umma su kara kula da tsaftar muhalin su da jikin su dan kaucewa kamuwa da cutuka.
Covid-19: Kungiyar likitoci NMA ta raba kayan kare kai
Covid-19: NMA ta bukaci membobinta da suka tsindima yajin aiki da su dawo aiki
Dakta Sanusi Muhammad ya kuma kara da cewar akwai bukatar samar da dakunan kwaje-kwaje a nan Kano domin ganin an inganta harkar lafiya duba da halin da ake ciki duk da cewar gwamnatin tarraya ta bada umarnin samar da dakunan gwajin a wasu jahohi.
Ana sa bangaran Khalid Sanusi Kani dalibi mai karantar fannin likata a Jami’ar Bayaro dake nan kano bayyana cewa yai a matsayin su na dalibai za su gudanar da tsare-tsare don kara wayar da kan al’umma game da cutar ta corona duba da cewar har yanzu akwai wanda basu yadda da ita ba.
Bakin sun kuma yi kira ga jama’a su kasance masu bin sawarwarin likitoci dan ganin an kaucewa kamuwar cutar ta Corona.
You must be logged in to post a comment Login