Labarai
NNPC zai fara aikin yashe tafkin Chadi da ya Santana ruwa yankin Gongola
Kamfanin mai na kasa NNPC ya ce nan gaba kadan ne za’a fara yashe tafkin Chadi da ya dangana zuwa yankin Gongola ya bi ta Benue bayan da kamfnain ya sami goyan baya daga rundunar sojan kasar nan don kare ma’ikatan sa.
Shugaban kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci manyan hukumomin kamfanin da suka kai zaiyara ga hafsan hafsoshin kasar nan Janaral Gabriel Olonisakin a ofishin sa dake Abuja.
Male Kyari ya bukaci al’ummar kasar nan da kada su siyasantar da batun yashe tafkin chadi , yayin da kamfanin ke amfani da dokar ’yancin bada bayanai
Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC ya kara da cewar sun kai ziyarar ne don neman goyan bayan rundunar sojan kasar nan baya wajen aikin yashe tafkin chadin.