Kiwon Lafiya
NNPC:ya sanya hannu kan takardar fahimtar juna da jami’ar Bayero
Kamfanin mai na kasa NNPC ya sanya hannu kan takardar fahimtar juna don gina babban sashen nazarin Civil Engineering a jami’ar Bayero dake nan Kano.
Ana sa ran aikin ginin zai lakume kudi da ya fiye da naira milyan dari uku da casa’in da bakwai.
Uban jami’ar Farfesa Muhammad Yahuza Bello da ya samu wakilcin mataimakin san a harkokin mulki Farfesa Haruna Wakili yay aba da kokarin kamfanin mai na kasa NNPC da suka jima suna bukatar hakan, inda yace jami’ar zata ci gaba da yin hadaka da NNPC wajen ciyar da jami’ar gaba.
Farfesa Haruna Wakili ya kuma bukaci ‘yan kwangilar dasu maida hankali wajen yin aiki mai nagarta kamar yadda aka san jami’ar wajen yin sabbin gine-gine masu inganci.