Connect with us

Labarai

NNPP ta ce ba za ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba

Published

on

Jam’iyyar NNPP ta sanar da cewa ba za ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba, tana mai cewa burinta shi ne haɗa kan jam’iyyun adawa domin ceto ƙasar daga matsalolin da take fuskanta.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, shugaban jam’iyyar na ƙasa, Bala Yusuf, ya bayyana hakan ne a taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da aka gudanar a Abuja, inda ya ce NNPP a shirye take ta kulla ƙawance da kowace jam’iyya da ta fito da ɗan takara nagari kuma mai hangen nesa.

Ya kuma musanta rahotannin da ke cewa jam’iyyar ta riga ta shiga wata haɗaka da wasu jamiyyun siyasa, ciki har da African Democratic Congress (ADC), yana mai cewa za su fara tantance ‘yan takarar da sauran jam’iyyu za su gabatar kafin yanke shawarar wanda za su mara wa baya.

Matakin na NNPP ya zo ne bayan ficewar manyan jiga-jiganta daga jam’iyyar, ciki har da Rabiu Musa Kwankwaso, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da wasu zaɓaɓɓun jami’ai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!