Labarai
Shugaba Tinubu ya tura tawaga zuwa Oyo bayan sace ɗalibai da malamai

Shugaba Bola Tinubu ya tura wata babbar tawaga ta gwamnati zuwa ƙauyukan Esiele da Yawota da ke yankin Ogbomoso a Jihar Oyo bayan sace ɗalibai da malamai kusan 46.
A cewar Jaridar DailyPost, tawagar ta ƙunshi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Tunde Disu.
Sauran mambobin tawagar sun haɗa da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe; da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Hulɗa da Jama’a, Sunday Dare.
Tun da fari dai wasu ƴan ta’adda sun kai hare-hare lokaci guda a makarantu biyu na Baptist Nursery da Primary School inda suka yi garkuwa da ɗalibai da malamai kusan 46.
A gefe guda kuma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da daukar masu gadin daji 1,000 a jihar Oyo, tare da umartar rundunar tsaro ta musamman mai kwarewa a ayyukan ceto ta kara kaimi wajen kubutar da dalibain.
You must be logged in to post a comment Login