Labarai
Al’hazan jihar Jigawa zasu fara dawowa gida Najeriya a mako mai zuwa

Mahajjatan Jihar Jigawa da suka halarci aikin Hajjin 2026 za su fara komawa gida daga ranar 6 ga watan Yuni, kamar yadda Amirul Hajj na jihar kuma Sarkin Dutse, Muhammad Hameem Nuhu Sunusi, ya sanar. Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa mahajjatan jihar da ke zaune a Makkah bayan kammala ibadun Hajji.
Sarkin ya yaba wa mahajjatan bisa yadda suka nuna ladabi, haƙuri da bin dokokin aikin Hajji, tare da ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da kiyaye dokokin jiragen sama yayin shirye-shiryen komawa gida. Ya kuma gargade su da kada su wuce adadin kayan da aka amince su ɗauka domin kauce wa matsaloli a filin jirgin sama.
Haka kuma, ya taya su murnar samun damar cika ɗaya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar, tare da roƙonsu da su ci gaba da yi wa Jihar Jigawa da Najeriya addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai, ci gaba da samun shugabanci nagari.
You must be logged in to post a comment Login