Labarai
Noma: matasa za su iya dawo da tattalin arzikin kasar nan ta hanyar Noma – IITA
Cibiyar bincike Kan harkokin noma a kasashe masu zafi IITA ta ce, shigowar matasa a harkokin noma zai farfado da tattalin arzikin Najeriya.
Shugaban cibiyar Dr Kenton Dashiell ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da manema labarai, a wajen taron wayar da kan matasa kan harkokin noma.
Dr Kenton Dashiell ya ce, taron zai taimaka wajen wayar da kan matasa kan mahimmanci noma don samar da yabanya mai kyau.
“Matasa su ne kashin bayan kowace al’umma, don haka matukar suka rungumi noma za a samu ci gaba”.
Dr Kenton Dashiell ya kuma ce, akwai abubuwa da za su fitar don tallafawa matasa a kan harka noma.
You must be logged in to post a comment Login