Kiwon Lafiya
NPC;Ta ce adadin al’ummar kasar nan ya kai miliyan dari da casa’in da takwas
Hukumar kidaya ta kasa NPC ta ce a yanzu haka adadin al’ummar kasar nan ya kai miliyan dari da casa’in da takwas, inda adadin al’ummar da ke rayuwa a birini ke karuwa da 6.5.
Shugaban hukumar kidayar ta kasa Mista Eze duruiheima ne ya bayyana haka a can kasar Amurka lokacin da ya ke bayani yayin taron tattauna batun yan gudun hijira da tattauna batun adadin al’ummar duniya karo na karo na 51
A cewar sa har yanzu Najeriya ita ce ke kan gaba a nahiyar Afrika wajen adadin al’umma, inda take kuma a mataki na bakwai a duniya duba da cewar yanzu al’ummarta ta kai miliyan 198.
Ya kara da cewa a hasashen da akayi nan da shekarar 2050 kasar nan za ta zama kasa ta uku a fadin duniya da ta fi kowacce kasa al’umma.
Ya kuma ce cikin shekaru 50 da suka wuce adadin al’ummar da ke rayuwa a birni ke karuwa, inda kowacce shekara ke karuwa da kaso 6.5 ba tare da karuwar ababen more rayuwa ba.