Connect with us

Labarai

NUJ ta goyi bayan rundunar Soji na yin aiki tare

Published

on

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa a Najeriya ta yi maraba da wani shiri da gwamnati ke duba yiwuwar aiwatarwa na bai wa ‘yan jarida damar bin tawagogin sojoji yayin da suke gudanar da ayyukansu a fagen daga, a wani mataki da ake ganin zai iya sauya yadda ake bayar da rahoto kan yakin da ake yi da ta’addanci a kasar.

Shirin na daga cikin kokarin gwamnatin Najeriya na inganta sahihancin rahotannin da ake samu daga yankunan da ke fama da rikici, tare da nuna irin kalubalen da jami’an tsaro ke fuskanta a yayin gudanar da ayyukansu na yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai da kuma sauran barazanar tsaro da ke addabar sassa daban-daban na kasar.

An bayyana wannan kudiri ne a cikin wata sanarwa da Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya karanto a wani taron tattaunawa da kungiyar ‘yan jarida ta kasar.

A cewar sanarwar, gwamnati na duba hanyoyin da za su tabbatar da cewa ‘yan jarida za su samu damar yin aiki a fagen fama cikin tsari, ba tare da tauye ka’idojin tsaro ba, tare da tabbatar da cewa rahotannin da ke fitowa daga wuraren da ake gudanar da ayyukan soji sun kasance masu inganci.

Shugaban kungiyar ta NUJ na kasa, Alasan Yaya, ya bayyana goyon bayan kungiyar ga wannan yunkuri, yana mai cewa hakan zai iya taimakawa wajen kara fahimtar da jama’a kan kokarin da hukumomin tsaro ke yi a fannin yaki da rashin tsaro a kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!