Connect with us

Labarai

PRP ta zargi Sanata Kwankwaso da yi Mata zagon kasa

Published

on

Jam’iyyar PRP ta zargi tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da yi Mata zagon kasa ta hanyar siyan form ga ‘yan takarar Jam’iyyar a Jiha, duk da cewar shi ba dan Jam’iyyar ba ne.

 

Shugaban kungiyar  masu Ruwa da tsaki na Jam’iyyar wato stakeholders forum Alhaji Abdulkadir  Musa Guza, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da Jam’iyyar ta gudanar yammacin jiya Lahadi.

 

Alhaji Abdulkadir Musa Guza, ya ce a kalla ‘yan takarar jam’iyyar 69, gaba daya aka siye form din su da abin ba iya Jam’iyyar ya tsaya ba har da wasu jam’iyyun suma da ake musu barazanar kwace jam’iyyun su da lalata su.

                                       

Shugaban ya ce zasu yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun yaki abinda aka zo musu dashi tare da saita Jam’iyyar su , wanda in har abun ya ci tura zasu dauki matakin shari’a da wanda suke zargin, tare da bayyana hujjojin da suke da su a hannu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!