Labarai
Obasanjo ya yi suka kan albashi da kuɗaɗen da ƴan majalisar tarayya ke karɓa

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya soki albashi da kuɗaɗen gudanarwa da ’yan majalisar tarayya ke karɓa, yana mai cewa bai dace a rinka biyansu wadannan kudaden ba a ƙasar da ake biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Obasanjo Ya zargi ’yan majalisar da tsara yanayin albashinsu da kansu, wanda ya ce ya sabawa kundin tsarin mulkin ƙasar. Ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi a wata tattaunawa ta yanar gizo ta The Toyin Falola Interviews, karkashin jagorancin Toyin Falola.
A wajen taron, an kuma samu mahalarta irin su The Kukah Centre wanda Matthew Kukah ya wakilta, da tsohon dan takarar shugaban ƙasa Kingsley Moghalu, yayin da Obasanjo ya kwatanta kasafin majalisar yanzu da na 2007, yana cewa bambancin yana da yawa kuma abin mamaki ne.
You must be logged in to post a comment Login