Labarai
Onuachu ya lashe lambar yabo ta takalmin Ebony
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Paul Onuachu ya lashe kyautar dan wasan da yafi kowa zura kwallo a ‘yan wasan Afrika dake taka leda a nahiyar Turai.
Yanzu haka dai Onuachu ya na taka leda ne a kungiyar kwallon kafa ta Genk dake kasar Belgian.
Dan wasan mai shekara 27 ya yi nasarar jefa kwallo 33 a gasar ajin kwararru ta Belgian wato Pro-League da aka kammala a bana.
Onuachu ya zama dan Najeriya na farko da ya lashe kyautar bayan shekaru 25 da Celestine Babayaro ya taba samun kyautar yayin da yake buga wasa a kungiyar Anderlecht a 1996.
You must be logged in to post a comment Login