Connect with us

Labarai

CAN ta yi maraba da ceto ɗaliban Oyo da aka sace

Published

on

Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bayyana farin cikinta kan ceto ɗalibai, malamai da sauran mutanen da aka sace daga makarantu a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo, bayan sun shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa. Ƙungiyar ta ce wannan abin godiya ne ga Allah, tare da taya iyalan waɗanda aka ceto murnar sake haɗuwa da ‘yan uwansu.

Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, rundunonin soji, ‘yan sanda, DSS, jami’an Amotekun, mafarauta da masu sintiri saboda rawar da suka taka wajen nasarar aikin ceto. Haka kuma ya jinjinawa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, bisa goyon bayan da ya bai wa iyalan waɗanda aka sace da kuma alƙawarin kula da lafiyarsu bayan dawowarsu.

Sai dai CAN ta ce har yanzu akwai dubban iyalai a jihohin Borno, Neja da sauran sassan Najeriya da ke jiran a kuɓutar da ‘yan uwansu da ke hannun masu garkuwa da mutane. Ƙungiyar ta bukaci gwamnati ta ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda ake tsare da su, tare da samar musu da kulawar lafiya da ta tunani bayan an kuɓutar da su, tana mai jaddada cewa ya kamata makarantu su kasance wuraren ilimi ba wuraren tsoro ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!