Labarai
PDP ta dakatar da wasu mambobin ta a jihar Kano

Shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano, Alhaji Yusuf Ado Kibya, ya sanar da dakatar da mambobi uku na jam’iyyar bisa zargin aikata laifukan da suka sabawa kundin tsarin PDP da manufofinta. A cikin sanarwar da ya fitar a jiya talata, ya ce jam’iyyar ta gano wasu ayyuka, dabi’u da halaye daga wasu mambobi da suka karya doka da oda, ciki har da shiga harkokin jam’iyyar adawa, aikata ayyukan da ka iya zubar da mutuncin jam’iyyar, da kuma aikata almundahana.
Alhaji Yusuf Ado Kibya ya bayyana cewa, a wani taro da kwamitin zartarwar jam’iyyar PDP Kano ya gudanar a ranar 15 ga Disamba, 2025, an yanke shawarar dakatar da mambobin uku gabanin kammala bincike da ɗaukar mataki na ƙarshe. Wadanda abin ya shafa sun hada da Ibrahim Bala Aboki daga Karamar Hukumar Nassarawa, Injiniya Bello Gambo Bichi daga Karamar Hukumar Bichi, da Rabiu Wangal daga Karamar Hukumar Nassarawa. Ya ce an dakatar da su nan take bisa tanadin sashe na 58 na kundin tsarin PDP da aka yi wa gyara a shekarar 2017.
You must be logged in to post a comment Login