Labarai
PDP ta kara wa’adin mayar da fom din neman shugabancin jam’iyyar a matakin jihohi
Kwamitin gudanar da ayyukan jam’iyyar PDP ta kasa ya kara wa’adin mayar da takardun takarar shugabancin jam’iyyar a matakin jihohi, zuwa ranar 1 ga watan Oktoba maimakon 23 ga watan Satumba da aka sanya a baya.
Mai magana da yawun jam’iyyar na kasa Kola Ologbondiyan, shi ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
A cewar shi, jihohin da abin ya shafa sune Adamawa da Borno da Ebonyi da Kebbi sai Kwara da Lagos da kuma Oyo.
Ya kara cewa hukuncin da Kwamitin ya yi, ya dace da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka gyara a 2017.
You must be logged in to post a comment Login