Labaran Wasanni
Pep Guardiola ya lashe gwarzon masu horaswa na duniya
An bayyan gasar firimiyar kasar ingila a matsayin wacce ke kan gaba a jerin gasar manyan kasashe a duniya.
Hakan na zuwa ne bayan da aka ayyana sunayen masu horas wa guda hudu daga kasar ta ingila wanda suka fi kowa yin bajinta a duniya.
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Guardiola shine akan gaba, sai Thomas Tuchel na Chelsea a mataki na biyu yayin da Jurgen Klopp na Liverpool a matsayi na uku, Antonio Conte na Tottenham a na hudu.
Guardiola mai shekaru 50, ya jagoaran ci City lashe gasar firimiya karo na biyar a kakar wasan da ta gabata, inda kuma ya kai su wasan karshe na gasar zakarun nahiyar turai, wanda sukayi rashin nasara da ci daya da nema a han nun Chelsea, tare da lashe gasar League-cup har sau takwas.
Thomas Tuchel wanda ya karbi kungiyar Chelsea a kasa da wata biyar ya kasance a mataki na biyu. Inda ya lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.
Sai mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp shi ne ya kasan ce na uku, duk da Kasan cewar babu wani Kofi da ya lashe a kakar wasa ta 2020-2021.
Bayan nasarar da ya samu a gasar Serie A da kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, Antonio Conte an bayyana a matsayi na hudu, in da yake fatan ya ciyar da kungiyar sa ta Tottenham gaba zuwa karshen wannan kakar wasanni.
Tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich sannan mai horas da tawagar kasar Jamus a yanzu Hans-Dieter Flick shi ne a na biyar yayin da Roberto Mancini ke biye masa baya a matsayi na shida bayan da ya jagoran ci kasar Italiya lashe gasar nahiyar turai ta Euro 2020
You must be logged in to post a comment Login