Labarai
PHIMA da SAVICOM sun hada hannu don inganta ayyukan lafiya a Kano
Hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu a Jihar Kano wato PHIMA ta hada hannu da hukumar kula da da’ar ma’aikata wato servicom dan inganta aikin hukumar ta.
Shugaban hukumar ta PHIMA professor salisu Ahmad ibrahim ne ya bayyana haka yayin taron hukumar a lokacin da hukumar servicom takai masa ziyara.
Professor salisu Ahmad ya kara da cewa ‘sun gayyace SAVICOM domin su tattauna akan ayyukansu musamman yadda cibiyoyin lafiya masu zaman kansu suke gudanar da aikinsu.
Wanda ya ce ‘duba da irin korafe-korafe da suke karba daga al’umma ta yadda wasu cibiyoyin lafiya suke kula da su, don hada hannu da servicom din domin samun dai-daito a cibiyoyin lafiya’.
A nasa jawabin tun farko Daraktan SAVICOM Aminu imamu Wali cewa yayi ‘dalilin zuwan su shi ne su kulla alaka ta aiki domin inganta kwazan ma’aikatan hukumar’.
Yayin taron an tattauna batutuwa da dama don inganta aiki hukumomin a jahar kano’
You must be logged in to post a comment Login