Labaran Wasanni
Pillars ta kaddamar da sabon mai horas wa daga Faransa
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta kaddamar da sabon mai horaswa dan kasar Faransa Lione Emmanuel Soccia da wasu ‘yan wasa 9 da zasu wakilceta a gasar cin kofin kwararru na kasa da kuma gasar cin kofin kalubale na Afrika a kakar wasa mai zuwa ta 2020/2021.
An dai gabatar da sabon mai horas war ga manema labarai a nan Kano, inda mahukuntan kungiyar da masu ruwa da tsaki a harkokin kwallon kafa suka shaida.
Shugaban kungiyar ta Kano Pillars Alhaji Surajo Yahaya Jambul ya ce “Pillars ta zabi baturen dan kasar Faransa ne duba da kwarewarsa a fanin wasannin kwallo a nahiyar Afrika tare da daukar sa kwantiragin shekara daya don kaiwa ga ci”.
Haka kuma shima Soccia ya ce “Zan yi iya bakin kokarina wajen kawo ci gaban Kano Pillars tare da ganin mun lashe duk wata gasa dake tafe.”
‘Yan wasa da kungiyar ta dauka guda 9 sun hadar da: Mustapha Jibrin daga Niger sai Jerome Heutchou daga Afrika ta Kudu sai Munkaila Musa daga jihar Yobe sai Frank Laura Cocoa daga Jamhuriyar Benin sai kuma Nnaji David daga Elkanemi Warriors da sauran su.
You must be logged in to post a comment Login