Labaran Wasanni
PSG tayi nasara da ci 1-0 a kan Real Madrid

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain tayi nasarar doke Real Madrid da ci 1-0 a wasan gasar cin kofin zakarun turai Champions League.
Fafatawar da ta gudana a ranar Talata 15 ga Fabrairun 2022 a filin wasa na Parc des Prince da ke kasar Faransa.
‘Yan wasan PSP da na Real Madrid
Dan wasa Klian Mbappe ne ya zura kwallo daya tilo a ragar Real Madrid a minti na 94 dab da za a tashi daga wasan.
Wasan dai shi ne na farko a zagaye na 16 na kungiyoyin da ke fafatawa a gasar ta kakar wasannin shekarar 2021/2022.
A wasa na gaba dai Real Madri zata karbi bakuncin PSG a filin wasa na Santiago a ranar 9 ga maris mai zuwa.
A daya wasan da aka gudanar dai Manchester City ta lallasa Sporting Lisbon da ci 5-0 a wasan da suka fafata.
You must be logged in to post a comment Login