Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Qatar 2022: Jamus ce kasa ta farko data samu tikitin buga gasar cin kofin Duniya

Published

on

Kasar Jamus ce kasa ta farko data samu tikitin buga gasar cin kofin Duniya da za’a gudanar a shekara mai kamawa ta 2022 a kasar Qatar

Hakan na zuwa ne bayan lallasa kasar North Macedonia da ci 4-0 a wasanni share fagen buga gasar a jiya.

Dan wasan kasar Jamus Kai Harverts ne ya fara zura kwallo a wasan a mintuna na 50 sai kuma Dan wasa Timo Werner ya jefa kwallo biyu a mintuna na 70 da 73 yayin da dan wasa Jamal Musiala ya ci kwallo ta hudu a mintuna na 83.

Da wannan nasara ce yasa kasar Jamus zama kasa ta farko data samu tikitin buga gasar cin kofin Duniya da za’a gudanar a kasar Qatar a shekara mai kamawa ta 2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!