Rahotonni
Rahoto : Halin da makarantun masu bukata ta musamman ke ciki a Kano
Daga wakiliyar mu Bushra Hussain Musa
A makon da ya gabata ne dai daliban makarantun furamare da sakandare suka koma makaranta bayan da gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarni.
Freedom Radio ta bibiyi wasu makarantun don ganin halin da suke ciki.
Makarantar firamare hade da sakandare ta masu bukata ta musamman dake Tudun-Maliki a nan Kano, na daya daga cikin makarantun da gwamnatin jihar ta samar don koyar da masu bukata ta musamman ilimin zamani.
A ziyarar da muka kai wannan makaranta mun gano daliban makarantar na fuskantar kalubalen rashin kujerun zama da kuma matsalar bandakuna, baya ga lalacewar azuzuwan da suke daukar darasi a ciki.
A gefe guda kuma akwai tarin shara da ta yi wa makarantar kawanya, wadda ke barazana ga lafiyar daliban har ma da malamansu.
A watan satumbar da ya gabata ne gwamnatin jihar Kano ta ware wasu kudade don gyaran makarantu, inda aka baiwa ko wace makaranta naira miliyan 20 don samar da kyakkyawan yanayin koyo-da- koyarwa.
To ko wane kokari gwamnati ke yi a bangaren ilimin dalibai masu bukata ta musamman a jihar Kano? Muhammad Sanusi Sa’idu kiru shi ne kwamishinan ilimi na jihar Kano, ya yi mana karin kan wannan batu.
Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ya ce, nan gaba kadan makarantar masu bukata ta musamman za ta zamo abin kwatance a jihar Kano, domin kuwa tuni shiri ya yi nisa na kawo karshen matsalolin da suke fuskanta.
You must be logged in to post a comment Login