Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Rahotonni

Rahoto : Shigowar makarantun boko ya dakushe yaduwar harsuna a Najeriya – Farfesa

Published

on

Daga Mu’azu Tasi’u Abdurrahman

Wani malami a sashen nazarin kimiyyar Harsuna a Jami’ar Bayero dake nan Kano, ya ce, shigowar makarantun boko a kasar nan ya taimaka wajen dakushe yaduwar bunkasar harsunan da ake da su a fadin kasar nan.

Farfesa Mukhtar Yusif ne ya bayyana hakan ta cikin shirin duniyar mu a yau na nan tashar freedom rediyo da ya mayar da hankali kan kalubalen da wasu harsunan kasar nan ke fuskanta ta fuskar karancin masu magana da harshen uwa.

Farfesa Mukhtar Yusif ya ce barin magana da wani harshe da masu magana da shi ke yi ya kan taimaka wajen durkushewarsa ko kuma gushewarsa baki daya daga doron duniya, kamar yadda yake wakana a yanzu kan wani harshe da yake dab da shirin mutuwa a kudancin kaduna.

Shi ma da ya kasance a cikin shirin Malam Musa Yahya ya ce gwamnatocin kasar nan su ne suka bada gudummawar dakushewar wasu harsuna a kasar nan.

A nasa bangaren Mal Isa Ado Ahmad na sashen nazarin tarihi a Kwalejin nazarin shari’a da addinin musulunci dake nan Kano, ya bayyana cewa hijira ko kuma kaura daga wani wuri zuwa wani wuri na taimakawa wajen gushewar wani harshe daga bakin al’umma.
Daga cikin harsunan da ke fuskantar barazanar mutuwa kamar yadda bakin suka bayyana ta cikin shirin Duniyarmu A Yau sun hada da yaren Tibi da Kambari da Atayam da dai sauransu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!