Kasuwanci
Rahoto: tsadar man fetur ya haifar da dogon layi a gidajen mai
A ƴan kwanakin nan dai an ga yanda ake fuskantar matsala ta karan cin man fetur a faɗin kasar nan, wanda ba’a san dalilin faruwar hakan ba.
Rabon da a fuskanci wannan matsala dai tun kusan shekara shida baya a shekarar 2015.
A zagayen da Freedom Radio ta gudanar a cikin kwaryar birnin, wakilan mu sun nazarci yadda wasu gidajen mai suke a rufe.
Yayin da wasu kuma suke a bude sai dai a kwai dogon layi mai tsayi.
A gefe guda kuma an lura da wasu gidajen man suka mayar da hankali kan sayar da man ga masu sana’ar bunburutu.
Sai dai yayin da ake tsaka da fuskantar karancin mai a wannan lokaci, wani rahoto da kamfanin man fetur na kasa NNPC ya fitar ya nuna cewa Najeriya ta kashe naira biliyan 864 wajen bada tallafin man fetur a cikin watanni takwas na shekerar da muke ciki.
Rahoton wanda hukumar kula da arzikin kasa ta fitar a watan Oktoba, ya nuna cewa an kashe kudin ne daga watan Fabarairu zuwa Satumbar shekarar nan.
Sai ga shi a wannan lokacin da al’umma suke cikin matsin rayuwa, kuma suna fuskantar tsadar man fetur da karancin sa.
You must be logged in to post a comment Login