Kiwon Lafiya
Rahoto: Yadda shara ke barazanar lalacewar titin jirgin ƙasa a Kano
Wani al’amari da ake ganin barazana ce ga muhalli shi ne yadda ake zubar da shara akan layin dogo musamman ma idan ya ratsa ta cikin unguwanni.
Tuni dai hukumomi ke gargaɗi kan zubar da bola akan hanyar da jirgin ƙasa ke wucewa sakamakon hatsarin da zai iya haifarwa.
A cewar masana muhalli ma zubar da shara barkatai barazana ce ga lafiyar al’ummar da ke rayuwa a yankin, kuma zai iya janyo hatsarin jirgin ƙasan idan da tsautsayi.
A zantawar mu da wasu daga mazauna unguwannin da layin dogon ya ratsa irin su Sharada, Gandu da sauran su, sun bayyana cewa..
Malam Shehu Ibrahim da ke zaune a Sharaɗa gidan Maza ya ce “Mazauna unguwar ne suke zubar da shara, amma wani lokacin akwai ƙarancin guraren zubar da sharar shiyasa ake zubarwa ko’ina”.
Shi kuwa Malam Jibrila Ya’u mazaunin unguwar Gandu cewa yayi “A lokacin baya wasu daga cikin mutanen unguwar suna hanawa ,amma daga baya da suka gaji suka daina sabida akwai ƙarancin guraren zubar da shara”.
Malam Umar shi ma ya ce “Muna sane da illar zubar da shara akan titin jirgin ƙasan, amma babu yadda za mu yi ne shiyasa muke zubarwa a duk inda muka samu, kuma hakan zai ƙara janyo hankalin gwamnati ta san matsalar mu”.
Sai dai mazauna unguwannin sun buƙaci gwamnati ta kawo musu babban abin zuba shara ko kuma hukumar kula da titin jirgin ta kawo musu don kiyaye matsalar zubar da sharar.
You must be logged in to post a comment Login