Labarai
REMASAB ta gargaɗi masu sayar da kayayyaki a gefen tituna

Hukumar Kula da Kwashe Shara da Tsaftar Muhalli ta Jihar Kano REMASAB ta gargadi masu sana’a da sayar da kayayyaki a gefen tituna da su daina zubar da shara a kan tituna da cikin magudanan ruwa.
Daya daga cikin daraktocin hukumar, Dr. Muhammad Salisu Khalil ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, zubar da bawon masara ko kwanson masara da sauran tarkace na iya toshe magudanan ruwa tare da lalata tsaftar muhalli.
A cewarsa hukumar na gudanar da ayyukan share tituna da kwashe shara akai-akai, amma wasu masu sana’a kan sake zubar da shara bayan an kammala aikin, dakta Khalil ya kuma ce, hakan na tauye kokarin gwamnati wajen samar da tsaftataccen muhalli da kare lafiyar al’umma.
REMASAB ta ce za ta ci gaba da aiwatar da dokokin tsaftar muhalli, inda duk wanda aka samu yana zubar da shara a wuraren da doka ta haramta zai fuskanci matakin da ya dace, ciki har da gurfanar da shi a gaban Kotun.
You must be logged in to post a comment Login