Labarai
Rahoton na musamman: kan ranar Damukradiya ta duniya
Masana da masu sharhi kan al’amuran dake gudana a Nijeriya sun ce babban kalubalen da kasar tafi fuskanta tun bayan fara gudanar da tsarin mulkin dimukradiyya shine rashin samar da ingantaccen ilimi da kuma bunkasa tattalin arziki.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake gudanar da bikin ranar dimukradiyya ta duniya a yau.
Bikin ranar dimukradiyya a bana ya zo ne a dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke bukatar cin moriyar dimukradiyyar, ta hanyar samar musu da ingantaccen ilimi da bunkasa fannin lafiya da tsaro da tattalin arziki da kuma kayan more rayuwa.
Wannan dai shine lokaci mafi tsaho da farar hula suka dade suna gudanar da mulki tunda Najeriyar ta samu yancin kai a shekarar 1960.
Tun bayan da farar hula ta karbi mulki, a iya cewa akwai bangarori da dama da aka samu ci gaba da kuma wuraren da aka samu nakasu wanda al’ummar kasar ke fatan shuwagabanni su kawo gyara don su ci moriyar dimukradiyyar.
Majalisar dinkin duniya ce dai ta ware duk ranar 15 ga watan satumbar ko wacce shekara a matsayin ranar dimukradiyya,da nufin karfafawa gwamnatoci gwiwa wajen gudanar da tsari da kuma mulkin dimukradiyya.
Taken bikin ranar a bana dai shine hada kai domin tallafawa a samar da ci gaba a karni na gaba.
Rahoton: Ummulkairi Abubakar Ungoggo
You must be logged in to post a comment Login