Labarai
Ranar ƴaƴa mata: wata ɗaliba ta ɗana kujerar gwamnan Kan
A yayin da ake bikin ranar ’ya’ya mata ta duniya, gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa wata ɗaliba damar zama a kan kujerar sa ta gwamna ta tsawon sa’a guda.
Dalibar mai suna Atika Aminu ‘Yankaba ta jagoranci zaman majalisar zartarwa ta Jiha tsawon sa’a guda tare da kwamishinoninta.
Da take zantawa da manema labarai bayan kammala zalamn, Atika Aminu ‘Yankaba ta ce sun tattauna kan matsalolin da suke damun al’ummar Jihar Kano, tare da zakulo hanyoyinmagance su.
Gwamnar ta Kano ta sa’a guda ta ce idan aka bai wa mata dama za su iya zama gwamna a nan Kano.
Ɗalibar mai shekaru 13 ‘yar aji uku a sakandare ta mayarwa gwamna kujerarsa, har ma Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yaba da yadda ta jagoranci zaman majalisar zartarwar.
Kafin taron, sai da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya halarci taron kungiyar alkalan kotunan majistire, wanda ya mayar da hankali kan irin rawar da bangaren shari’a zai taka wajen dakile aikata laifuka ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta na zamani.
You must be logged in to post a comment Login