Labarai
Ranar daukar hoto: Akwai marasa ƙwarewa a harkar – Ƙungiyanar daukar hoto:
Ƙungiyar masu ɗaukar hoto ta ƙasa reshen jihar Kano ta ce, harkar ɗaukar hoto na fuskantar matsala sakamakon shigar waɗanda ba su da ƙwarewa a harkar.
Shugaban ƙungiyar Abdulwahab Sa’id Ahmad ne ya bayyana hakan, jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan Freedom Radiyo, wanda yayi duba kan mahimmanci ranar dauka hoto ta duniya da ake gudanarwa a duk ranar 19 Agusta.
Abdulwahab ya ce, “Babban ƙalubalen ƙungiyar bai wuce yadda ma’ikatun gwamnati ke ƙin ɗaukar ƙwararrun masu ɗaukar hoto don su yi aiki tare da su ba”.
Guda daga cikin membobin kungiyar da ta kasance cikin shirin Hafsa Sani Muhammad ta ce, “Rashin isassun mata a cikin kungiyar koma baya ne a harkar”.
Sai dai ta buƙaci gwmanati da ta riƙa ɗaukar nauyin matasa wajen fitar da su guraren da za su koyi harkar gyaran kyamara musamman ma ta zamani.
You must be logged in to post a comment Login