Coronavirus
Ranar Lahadi za ayi Sallah a Zaria – Sarkin Zazzau
Maimartaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya ce ranar Lahadi itace ranar Sallah a garin Zaria.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu da Freedom Radio ta samu a daren Juma’a tace masarautar bata umarci al’umma su ajiye azuminsu a ranar Asabar ba.
Sanarwar ta kara da cewa Sarkin Zazza na umartar al’umma da suyi biyayya ga umarnin mai alfarma Sarkin musulmi wanda shine Allah ya dorawa hakkin bada sanarwar ganin wata, kuma tuni ya sanar za ayi sallah ranar lahadi.
A daren Juma’a ne aka rika yamadidi da wasu rahoronni a kafafan sada zumunta kan cewa Sarkin Zazzau ya bada sanarwar a ajjye azumi ranar Asabar.
You must be logged in to post a comment Login