Labarai
Ranar Ma’aikata: Ganduje ya yafe wa Malamai bashin kudin mallakar gidaje
Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta yafe wa Malaman makarantun da suka shiga tsarin mallakar gidaje ta hanyar biya a hankali daga albashinsu, ragowar kudin da ba su kammala biya ba.
Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya bayyana hakan a jawabinsa na bikin ranar ma’aikata na bana da aka gudanar a a filin wasa na Sani Abacha da ke unguwar Kofar mata da safiyar yau Litinin.
Ganduje ya kuma gode wa ma’aikatan jihar Kano bisa goyan baya da hadinkai da suka ba shi wajen gudanar da mulki na tsawon shekaru takwas.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar Kwadago ta Najeriya reshen jihar Kano kwamared Kabiru Ado Inuwa, ya ce a tasa mahangar matsalar fanshon wadanda ke barin aikin gwamnati sun fi wanda ake dauka yawa.
Taron dai, ya samu halartar kungiyoyin ma’aikata daga bangaren gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Rahoton: Abba Isah Muhammad
You must be logged in to post a comment Login