Labarai
Ranar ma’aikata: Gwamnati ta ayyana litinin 3 ga watan Maris a matsayin ranar hutu
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 03 ga watan Mayu, a matsayin ranar hutu a fadin kasar nan na bikin murnar ranar ma’aikata ta Duniya.
Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola,ne ya sanar da hakan ga manema labarai tare da godewa ma’aikatan kasar nan.
Ta cikin sanarwar da aka fitar yau Alhamis, da babban sakataren ma’aikatar Shuaibu Belgore ya fitar, Aregbesola, ya bukaci ma’aikatan da su kara jajircewa wajen gudanar da ayyukan su da gaskiya da zai bunkasa kasar nan.
Ministan ya kara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari na yin duk mai yiwuwa wajen samarwa da ma’aikata kyakkyawan tsarin gudanar da aiki, ciki har da kyautata tsaro a fadin kasar nan don samar da ci gaba mai dorewa.
You must be logged in to post a comment Login