Labarai
RanarHausa: An yi bikin ranar Hausa ta duniya a Rano
An gudanar da bikin ranar Hausa ta duniya wanda kungiyar al’ummar Hausawan duniya (AHAD) ƙarƙashin shugabancin Dakta Abdulkadir Labaran Koguna, ta shirya a Ƙofar tsohuwar Fadar Sarkin Rano, dake Rano a nan Kano.
Taron ya samu halartar ɗimbin al’umma daga sassa daban-daban na ƙasar nan da kuma maƙotan ƙasashe.
Taron wanda ya ƙunshi manufofi da dama da suka haɗa da al’ada da gargajiya da kuma samar da daidaitacciyar Hausa don gyara ƙa’idojin rubutu a Afirka da duniya baki ɗaya.
Sannan taron ya yi duba a al’amura daban-daban na rayuwar Bahaushe a zamanin da, dana yanzu, wanda ya tabbatar da maganar Hausa ta cewar yaren ya zama Ƙwaron Wake sai an ci da kai.
Farfesa Gangaran Abdulƙadir Ɗangambo, ya yi dogon jawabi kan matsalolin Hausawa da harshen, tare da bada shawarwarin magance matsalolin ciki har da sha’anin Bara da Almajirci da kuma Mari.
Shima a nasa jawabin, Dakta Abdullahi Garba Tudun Wazirci, malami a sashen Nazarin Harshen Hausa a kwalejin koyon aikin shari’a ta Aminu Kano wato Legal, yace bikin wannan rana ya nuna irin bunƙasar harshe, kasancewar cikin harsuna sama da dubu 6, a faɗin duniya harshen Hausa shi ne na 11.
Wakilin mu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito cewa, duk da bikin ya danganci al’adu na Hausawa, ba a samu sarkin yanka guda ɗaya daga cikin Sarakunan yanka biyar na Kano da ya halarci taron ba, sai dai Sarkin Rano ya aika da wakilci.
You must be logged in to post a comment Login